Abubuwan da kwalejin nazarin nahiyar Afrika ke
gudana a kwanan baya

Ci gaban da kwalejin ke samu a kwanan baya

Cibiyar Bincike Afirka ta jami’ar ba da ilmin koyo ta lardin Zhejiang cibiya ta farko ce dake cikin jami’a kan bincike Afirka ta kasar Sin. Ta zauna cikin birnin Jinhua na lardin Zhejiang dake gabas ta Sin. Burin kafa wannan cibiyar shi ne tattara masana masu nazarin Afirka dake kasashen ciki da waje don su ba da kokarinsu kan bincike Afirka. Haka kuma bayan wasu shekaru su zama wata kungiya mai zamani kan bincike Afirka a duniya, kuma samar da amfaninta ga diplomasiyar kasarmu da bunkasuwar jama’a da yankuna.

Akwai sassa hudu a cikin cibiyar wato sashen bincike Afirka kan siyasa da dangantakar dake tsakanin Afirka da kasashen duniya da sashen bincike tattalin arzikin Afirka da sashen bincike ilimin koyo na Afirka da sashen bincike tarihi da al’adun Afirka. Wadannan sassa hudu su mai da hankali kan batun bunkasuwar Afirka na zamani da dangankatar dake tsakanin Sin da Afirka da sauran makamatansu.

Mutane guda 23 suna aiki a cibiyar yanzu, daga cikinsu akwai shehu malamin gwamnatin Zhejiang duga daya da shehu malamai hudu, da mataimakin malamai biyar da masana masu digiri na uku guda 16, ban da wannan kuma akwai sauran malamai da masu bincike da yawansu ya kai 10 ko fiye. Sashen Afirka na ma’aitakar harkokin waje ta Sin da sashen yanke shawara na ma’aikatar da cibiyar al’adu da kimiyya ta Sin da kwalejin koyon ilimin diplomasiyya da sauran kungiyoyi sun nuna goyon bayansu ga kafuwar wannan cibiyar.

Mr. Liu Hongwu malami mai shahara kan bincike Afirka na kasar Sin kuma malami musamman na lardin Zhejiang ya dauki nauyin shugaba wannan cibiyar. Kuma mataimakin darekta na ofisin kula da harkokin waje na lardin Zhejiang Mr. Gu Jianxin ya zama mataimakin shugaban cibiyar.

Yanzu masanan Cibiyar Bincike Afirka su rigaya sun rubuta ilimin da aka samu daga bincike Afirka na jami’ar ba da ilimin koyo na lardin Zhejiang da mujallar cibiyar wato littafi bincike Afirka. Kuma ana shirin kafa cibiyar ba da shawara ga masu zuba jari ko yin tattalin arziki a Afirka. Ban da wannan kuma, akwai littatafai game da Afirka 5000 ko fiye a laburaren cibiya, yawan mujalla ya kai 90 ko fiye.

Daga shekarar 1990 zuwa shekarar 1999, jami’ar ba da ilmin koyo na lardin Zhejiang ta fara kafa cibiyar koyon harshen Sinanci a kasashen Afirka(wato Confucius Institute a yanzua ). A shekarar 2001, domin biyan bukatar ma’aikatar ba da ilmin koyo ta kasar Sin wato ba da taimako ga kasashen Afirka, jami’ar ta fara dauki nauyin gabatar da kwas din ga masu aikin dake game da Afirka, daga nan kuma, ta zama wani muhimmin wuri ta ma’aikatar ba da ilimin koyo ta Sin wajen taimaka wa kasashen waje. Cikin shekarar 2003, an kafa cibiyar bincike ilmin koyo ta kasashen Afirka a jami’ar, daga baya a shekarar 2006, an gudanar da taron dandalin tattaunawa na farko dake tsakanin shugabannin jami’o’in kasashen Afirka da Sin a jami’ar. Dadin dadewa a shekarar 2007, an kafa Cibiyar Bincike Afirka a hukunce. Bayan kokarin da aka yi cikin shekaru goma da suka wuce, kwalejin daban na jami’ar su ma sun kafa wasu kungiyoyi iri irin don nuna goyon bayansu kan bincike Afirka kamarsu cibiyar bincike waka ta Afirka da sauran makamatansu.

Cibiyar Bincike Afirka ta kafa dangantakar hadin gwiwa mai zumanta da jami’o’i 10 ko fiye na kasashen Afirka, kuma dalibai masu neman digiri na biyu da malaman cibiyar su kan tafi Afirka domin kara karatu a ko wace shekara. Yanzu, cibiyar ta sami dalibai masu neman digiri na biyu kan tarihin Afirka da comparative education.

Bayan kafuwar Cibiyar Bincike Afirka a shekarar 2007, an sami kyawawan sakamako masu dimbin yawa a cibiyar. A ran 12 ga watan Nuwanba ta shekarar 2008, an gudanar da taron bugawa littafin da masanan cibiyar suka rubuta mai suna Bincike Batun Darfur bisa halin da ake ciki yanzu a duniya a nan birnin Beijing. Kuma an gabatar da taron tattaunawa tsakanin kasa da kasa kan batun Darfur a ran nan. Sakamakon da masanan cibiyar sun samu wajen siyasa ta Afirka da tattalin arzikin Afirka da ilmin koyon Afirka ya jawo hankali sosai daga fannoni da bangarori daban daban.

Cibiyar Bincike Afirka ta zauna a gabas ta yamma dake jami’ar ba da ilimin koyo na lardin Zhejiang. Fadin cibiyar ya kai murabba’in mita dubu biyu ko fiye wadanda suka kunshe da dakin taro da dakin ganar da baki da makamatansu. Mu maraba mutanen da suke nuna babban sha’awa kan nazarin Afirka da su aiki a cibiyarmu.

Add: Cibiyar Bincike Afirka na jami’ar ba da ilmin koyo na lardin Zhejiang NO.688 na hanya

Yingbin na birnin Jinhua na lardin Zhejiang

Postal Code: 321004

Tel: +86 579 82286091

Fax: +86 579 82286091

Email: ias@zjnu.cn